Hausa

Muhimmin Bayani Akan Tallafin N50,000.00 Da Shirin Rance Da Gwamnatin Tarayya Ta Fara Bayarwa Ga Kananan Yan Kasuwa

Dafarko yana da kyau mu sani cewa shi wannan tallafin na gwamnatin tarayya ya kasu kashi biyu, kashi na farko shi ake kira grant wato tallafi. A wannan tsarin adadin tallafin dai ya kai N50,000.00 (naira dubu hamsin), kuma an tsara tallafin ne domin tallafawa masu kananan  sana’o’o miliyan daya a kananan hukumomi 774 da muke da su. A halin yanzu an rufe cike aikace-aikacen tallafin na farko kuma kuma gibi na farko ne suka samu tallafin, gibi na biyu kuma na cigaba da jiran nasu tallafin. Ana tsammanin za’a fara turawa wadanda basu samuba kwanannan, wasu jahohi kuma na cigaba da tan-tance BIO data na wadanda zasuci gajiyar shirin. Yanar gizo da zaku shiga: CLICK HERE

Tsarin tallafi/rance na biyu ana masa taken presidential palliative programmes transforming businesses, improving lives. A wannan tsarin yankasuwa manya, matsakaita da kanana ne zasuci gajiyar shirin, amma wannan tsarin bashi ne za’a bayar daga N500,000 zuwa N500,000,000 musamman ga yan kasuwa masu rijistar cac. Shi dai wannan tsarin yanada ruwa na 9% a duk shekara. Kuma har ayau ana ci gaba da cikewa ta yanar gizo kamar haka: CLICK HERE

Tsare-tsaren tallafi/rance

Kashi na farko

  • Sunan shirin: Presidential Conditional Grant Scheme (PCGS)
  • Shafin tallafi : CLICK HERE
  • Adadin tallafi: N50,000.00
  • Dole ne a samarda nin number kafin cikewa

Kashi na farko

  • Sunan shirin: Presidential Palliative Programmes Transforming Businesses, Improving Lives
  • Shafin tallafi: CLICK HERE
  • Adadin tallafi: N500,000.00 – N500,000,000.00
  • Dole ne a samarda nin number kafin cikewa