Hausa

Shirin Tallafi na SMEDAN x NJFP: Hukumar Raya Kanana da Matsakaitan Masana’antu ta Najeriya (SMEDAN) da Shirin Matasa na Jubilee Fellows na Najeriya (NJFP) sun Bude Sabon Shirin Bawa Matasa Tallafi

Hukumar Raya Kanana da Matsakaitan Masana’antu ta Najeriya (SMEDAN) an kafa ta a shekarar 2003 domin inganta ci gaban sashen kanana da matsakaitan masana’antu (MSME) domin haɓaka tattalin arzikin Najeriya. Shirin Matasa na Jubilee Fellows na Najeriya (NJFP) shiri ne na haɗin gwiwa da Gwamnatin Tarayyar Najeriya tare da Tarayyar Turai (EU). Hukumar Raya Kasa ta Majalisar Dinkin Duniya (UNDP) ke aiwatarwa.

Shirin an gina shine domin bawa matasa horo ta hanyar koya masu kasuwanci tsawon wata 12 tare da basu albashi/alawus mai tsoka da zasu iya rike kansu da iyalansu. An sama shirin suna “Shirin Haɓaka Baiwa na SMEDAN x NJFP”

yana haɗa ƙananan kamfanoni da ƙwararru. Wannan shiri na musamman daga Hukumar Raya Kasa ta Majalisar Dinkin Duniya (UNDP), yana tallafawa ƙananan kamfanoni da matasa hadi da basu alawus na tsawon wata 12.

APPLY HERE