Gwamantin tarayya ta fitar da adadin mutanan da su ka ci gajiyar shirin tallafi na N50,000.00 (Naira Dubu Hamsin
A halin yanzu dukan kananan Hukumomi 774 an fitar da yawan mutanan da suka amfana ni na fito ne daga karamar hukumar Makarfi mutum 59 ne suka samu tallafin 50k hakan ya nuna cewa gwamantin tarayya ko fara sakin Kuɗaɗen ba tayi ba ga alumma domin kowacce karamar hukumar dake najeriya mutum 1300 zasu amfana da shirin.
Adadin tallafin dai ya kai N50,000.00 (Naira Dubu Hamsin) ga kowane mai cin gajiyar tallafin, kuma an tsara shi ne don kaiwa ga masu sana’ar nano miliyan daya a kananan hukumomi 774.
Gwamnatin tarayya za ta hada kai da gwamnatocin Jihohi, NASME (Kungiyar Kananan Kamfanoni da Matsakaitan Masana’antu ta Najeriya),wadanda za su yi amfani da ka’idojin gwamnatin tarayya da ke kasa wajen tantance wadanda za su ci gajiyar shirin daga mazabarsu.
Wadanda ake shirin cin gajiyar shirin su ne kashi 70% na mata da matasa, kashi 10% na nakasassu, da kuma kashi 5% na manya, yayin da sauran kashi 15% aka raba ga sauran alkalumma.