Hausa
Labari Mai Dadi Akan Shirin Emergency Taskforce (EET)
A yau ne mai girma ministan kudi kuma mai kula da harkokin tattalin arziki ya mikawa shugaban kasa Bola Tinubu shirin samar da ci gaba a ofishin sa.
EMT Emergency Taskforce (EET) ce ta tsara shirin daidaita tattalin arzikin.
Shirin wani mataki ne na gwamnati tarayya ke yi don daidaita tattalin arzikin Najeriya da kuma mayar da shi zuwa wani babban yanayin ci gaba.
Kwamitin gaggawa na EMT ya ƙunshi mahalarta daga gwamnatin tarayya, gwamnatocin jihohi da kuma kamfanoni masu zaman kansu.