Aikin Karantarwa: Gwmnatin Jahar Jigawa ta Bude Shafin Daukar Malaman Sakandare
Karanta cikakken bayani na yadda za’a cike shirin J-TEACH da kuma k’aidojin da ake so mai nema shiga shirin ya cika, dole ne sai mai shaidar takaddar NCE a hannu wanda ya kamalla sune kawai aka sahale su nemi aikin(Recruitment guide).
1- Mataki na farko shine shiga ta wannan link https://subebjigawa.org.ng/recruitment/auth-login.php sai ayi creating account sai asa Name and surname, sai a sanya number waya, sai email address, sai a sanya NIN number .
2-Mataki na biyu sai a koma email address za’a ga an turama sak’o na application form number sai ayi copy na application form number a tafi mataki na uku..
3-Mataki na uku shine sai ka shiga abinda ake buk’ata shine abu biyu, wannan application form number da aka turama zaka d’auko a matsayin username naka, sai kuma kayi amfani da phone number ka a matsayin password, da shigarka zaka ga an bud’ema sak’on sannu da zuwa sai ka shigar da bayanan ka.
4-Mataki na hud’u idan ka shiga sai ka shigar da bayanan ka , wacce makaranta kayi ina aka haifeka da sauran bayanai..
5-Mataki na biyar sai a sanya bayanai da suka danganci karatu, ka gama primary, secondary, ka gama NCE da lokacin da kayi amma kayi dalla-dalla. Abin lura a kiyaye shine kafin a wuce kowanne mataki dole sai an cike na baya, misali idan ba’a cike wani abu ba a bio-data ba bayanan haihuwa , to ba zaka shige gaba ba zuwa matakin gaba sai ka shigar dole , dan haka a kiyaye a tanadi dukkan bayanan da ake buk’ata kafin a fara cikewa…
7-Mataki na bakwai shine sai a zab’i inda ake son a koyar za’a ga jerin makarantu jiha da ake dasu, zab’in mutum ne ya zab’i primary ko junior secondary amma duk wanda ya zab’i Junior ya tabbatar sakamakon NCE nashi yana da babban Grade. Idan kuma primary aka zab’a za’a ga jerin makarantu gwamnati a wurin selection acan inda aka shigar da bayanai, dole a sanar da ward naka da kuma inda kake zaune ward resident. Misali idan ace mace tana Auyo amma asalinta yar Hadejia.