A raba tallafin takin gwamnati kan lokaci don manoma su amfana – AFAN
A Najeriya, kungiyar manoman kasar ta All Farmers Association of Nigeria (wato AFAN) ta bayyana farin ciki game da takin zamani da gwamnatin kasar ta bayar ga gwamnatocin jihohi da ‘yan majalisar dokoki ta kasa.
Sai dai kuma tana ganin ya dace a yi rabon takin yadda ya kamata, kuma a kan lokaci, domin ya amfani manoman.
Honarabul Muhammad Magaji, sakataren watsa labarai na kungiyar manoman Najeriyar ya shaida wa BBC cewa su na da labarin takin da Ministan noma Sanata Abu Kyari ya raba wa gwamnonin jihohin kasar, kuma an yi rabon takin ne kan tsarin yawan manoman jiha – yawan takin da aka ba su.
‘Wadansu jihohin an ba su mota 65, wasu 35, wasu 25, har fiye da hakan, kuma abin da aka ba su ba na saidawa ba ne an bai wa manoma kyauta ne. Sannan su ma Sanatoci an ba su akalla mota bibbiyu, an bai wa ‘yan majalisar wakilan tarayya akalla mota daya kowannensu, su ma ministoci an ba su wannan taki domin su raba wa al’ummarsu kyauta, domin saukaka wa manoma tsadar kayan noma da tsadar rayuwa da ake fama da ita,” in ji Honarabul Magaji.
Magaji ya bayyana cewa daman sun jima da bayyana cewa akwai takin gwamnati, kuma sun roki a bai wa manoman kyauta, dan haka a yanzu an fara rabon takin a matakin gwamnatin jihohi.
- Manoma shinkafa na Kebbi sun zata tallafin Buhari kyauta ne25 Fabrairu 2020
- Gwamnatin Jigawa ta rage kuɗin takin zamani daga dubu 26 zuwa 1626 Yuli 2023
- Hotunan sabon kamfanin yin taki na Dangote22 Maris 2022
Magaji ya kara da cewa; ‘Duk wanda za a bai wa taki samfuri PK to yanzu ya kamata a ba da shi, saboda zai karfafa wa manoma, kuma zai saukar da farashin na kasuwa tun da za a same shi a wadace.
Muna rokon jihohi yadda mai girma shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da takin nan kyauta ta hannun ministan noma, kowacce jiha ta sayi nata ta hada da na gwamnatin tarayya domin bai wa manoma kyauta.
Su ma sanatoci damn su na ba da kayan aikin gona kyauta su kara taki haka ‘yan majalisa, domin samun wadataccen takin kuma kan tsarin tallafi zai ragewa manoma halin da suke ciki.”
Baya ga takin da gwamnatin tarayya ta bayar na tallafin, sun samu labarin akwai batun Hatsi da masara da shinkafa da aka raba wa jihohin Najeriyar akalla sama da mota 30, domin taimaka wa masu karamin karfi, shi ma Honarabul magajin ya yi kira ga gwamnonin su raba su a kan lokaci, hakan ne zai sanya farashin wanda ke kasuwa zai suka yadda za a samu sassauci kan halin da ake ciki.
Najeriya dai na fama da matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayan amfanin yau da kullum musamman na abinci, duk kuwa da noman da ake yi a kasar.
A bangare guda kuma matsalar tsaro da ake fama da ita musamman a wasu jihohin arewacin kasar ta tilasta wa manoma daina zuwa gonaki saboda tsoron kar ‘yan bindiga masu neman kudin fansa su yi garkuwa da su.