Save 20% off! Join our newsletter and get 20% off right away!

Yan Najeriya miliyan 70 za su samu N75,000 kowanne.

Yan Najeriya miliyan 70 za su samu N75,000 kowanne..

Gwamnatin tarayya ta kammala shirye-shiryen raba tsabar kudi Naira 75,000 ga ‘yan Najeriya miliyan 70 a wani yunkuri na rage radadin wahala.

Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin jama’a, Hon. Aliyu Audu, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, ya bayyana cewa matakin ya dace da kudurin gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu na magance matsalar talauci a kasar.

Audu, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC ta kasa kuma tsohon mamba a kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar APC, ya bayyana cewa Tinubu ya bayar da isassun hujjoji na nuna kwazo a cikin watanni 19 kacal da ya yi yana mulki.

Sabiu Danmudi Alkanawi